Mahaifiyar shahararren mawaƙin Hausa Dauda Kahutu Rarara, ta kuɓuta daga hannun ƴan bindiga bayan shafe mako uku a hannunsu.
Mawaƙin ne ya tabbatar da sakin Hajiya Hauwa’u Adamu a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram da safiyar yau Laraba.
An sace dattijuwar ne ranar 28 ga watan Yuni a ƙauyen Kahutu da ke ƙaramar hukumar Danja ta jihar Katsina.
“Cikin yarda da Amincin ubangiji, mun samu dawowar mama cikin aminci,” in ji shi. “Ina matuƙar godiya ga unbangijina.”
Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da ko an biya kuɗin fansa kafin sakin na ta.