Wata mata mai suna Zainab Ibrahim da ke unguwar Kpaduma ll da ke Asokoro a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Asabar din da ta gabata, ta mutu a yayin da ta ke raba fada da ya barke tsakanin ‘ya’yanta biyu, Inusa da Usman.
Rahotanni na cewa daya daga cikin ‘ya’yanta mai suna Inuwa ya yanki hannun mahaifiyarsu na hagu bisa kuskure.
Majiyar ta bayyana cewa, “An garzaya da Zainab wani asibiti mai zaman kansa inda ta rasu.”
Karanta Wannan: NDLEA ta kama mutane 25 a Abuja da zargin safarar kwayoyi
Ya ce Inusa ya yi yunkurin yin amfani da yankan da aka yi wa dan uwansa, amma bisa kuskure ya yanke mahaifiyarsa a hannunta na hagu.
Da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta bayyana cewa Inusa yana nan a hannun sa kuma ana ci gaba da bincike.
Ta ce rundunar ‘yan sandan ta samu kiran gaggawa kuma ta garzaya wurin da lamarin ya faru, inda ta jaddada cewa an kai mahaifiyar asibiti inda aka tabbatar da mutuwar ta.
Ta bayyana cewa Usman yana tsare, yayin da Inusa ke tsare.