Wata mata mai suna Fatima ta kai mahaifinta gaban kotun shari’a da ke zamanta a jihar Kaduna, saboda mahaifinta ya tilasta mata auren dole.
Fatima mai shekaru 20 ta shaida wa kotun cewa, tana da wanda take so amma mahaifinta, Aliyu Muhammad ya yi barazanar kai ta kauye ya aurar da ita.
Lauyan Fatima, Malam Bulama ya kuma shaida wa kotun cewa wanda yake karewa bai shigar da kara a kan mahaifinta ba saboda rashin girmama shi.
Bulama ya ce: “Uban yana son wanda nake karewa ya auri wani mutum a kauyensu da ke jihar Neja. A yanzu haka tana zaune a gidan auntynta domin ya yi mata barazanar zai kai ta kauye ya aure ta.
Shi ma a nasa bangaren, mahaifin Fatima, Aliyu Muhammad ya ce iyayensa da suka rasu sun zabi mijin ga diyarsa kafin rasuwarsu kuma ya mutunta bukatunsu.
“Na aurar da ‘ya’yana mata 6 a kauyen kuma suna nan lafiya. Mahaifiyar Fatima ita ce kwakwalwar da ke bayan taurin kanta. Ina bukatan izini domin in tuntubi jama’ata kan wannan al’amari,” inji shi.
Alkalin kotun, Isiyaku Abdulrahman, ya ce uba a karkashin dokar Shari’a, yana da hakkin ya zabar wa diyarsa mijin aure.
Sai dai ya lura cewa ba a karfafa auren dole.
“Kai ne mahaifinta, don haka ka ba ta damar gabatar da wanda take so ta aura, idan kuma kana son addininsa da halayensa ka yarda ta yi aure,” in ji kotun.


