Mahaifin tsohon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Wakili (Singam), Alhaji Buba Turaki, ya rasu a jihar Gombe.
Marigayin wanda ya kasance tsohon jami’in hukumar Kwastam ya rasu a safiyar yau Lahadi, 6 ga watan Fabrairu, An yi jana’izarsa da misalin karfe 2:00 na rana a kofar Fadar mai martaba Sarkin Gombe.
Ya rasu ya na da shekaru 106 a duniya bayan ya yi fama da rashin lafiya, kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito.
Alhaji Turaki ya rasu ya bar matan aure da ’ya’ya 10, maza biyar da mata biyar.