Wani mahaifi mai shekaru 60, Malam Bala da dansa, Sunusi Bala mai shekaru 35, sun nutse a ruwa ranar Laraba a Kano.
Mutanen biyu sun rasa rayukansu ne a Sabon Garin Bauchi, cikin karamar hukumar Wudil, a lokacin da suke kwashe ruwa daga rijiya.
Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Abdullahi, ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne da safiyar Talata.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Abdullahi ya ce, an kai wa ofishin kashe gobara ta Wudil da misalin karfe 11:30 na safe ta wani Isma’ila Idris.
“An kira wani uba da dansa domin su yashe rijiya, sun yi nasarar yashe ta.
“Amma, dan ya koma cikin rijiyar ya share ta a lokacin da ya makale ya shake.
“Mahaifinsa ya bi shi don ceto shi, lokacin da shi ma ya makale ya shake saboda rashin iskar oxygen a cikin rijiyar”, Abdullahi ya ce.
An fito da wadanda abin ya shafa daga rijiyar a sume kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsu.
Abdullahi ya kara da cewa, an mika gawarwakin ga Insp Felix Gowok na ofishin ‘yan sanda model na Wudil.