Gwamnatin tarayya ta jaddada ƙudirinta na samun ƙarin masu amfani da magungunan hana daukar ciki zuwa kashi 27 cikin 100 nan da shekarar 2024.
Babban Sakatare a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Daju Kachollom, ce ta bayyan haka a wajen buɗe taron shekara-shekara na kwana biyu da ƙungiyar ‘Society Family Health’s (SFH) Adolescent 360’ (A360-Amplify) ta shirya, don ƙara nazari game da amfani da magungunan.
Taron na mai taken: “ɗorawa a kan nasarorin da aka cimma a shirin bunƙasa lafiyar balagar masu tasowa a Najeriya”
Kachollom, wadda Darakta a sashen kula da lafiyar iyali, Dakta Stella Nwosu ta wakilta, ta ce wannan matakin ba wai manufa ce kawai ba, amma alƙawari ne ga matasan kasar.
“Wannan alƙawari ne na ƙarfafa matasa da ilimi da kayan aiki don yanke shawara mai kyau game da lafiyar jima’i da haihuwa”.
“Wannan shirin zai ba da fifiko mai ƙarfi kan Tsarin Dan Adam (HCD) da haɗa kai cikin tsarin kiwon lafiya da ci gaba na gwamnati.
“Shirin ya samo asali ne ta hanyar fahimtar gamayyarmu cewa, za a iya samun tasiri mai ɗorewa ta hanyar hada kai don tabbatar da “ɗorawa a kan nasarorin da aka cimma a shirin bunƙasa lafiyar balagar masu tasowa a Najeriya” ba tare da wani tangarɗa ba cikin yanayin kiwon lafiya.
Kamfanin Dillancin Labarai na (NAN), ya ruwaito cewa, taron ya ba da dama ga abokan tarayya da kuma masu ruwa da tsaki daga bangarorin gwamnati da masu zaman kansu don yin tunani kan sabbin hanyoyin da za a bi don dorewar shirin.


