fidelitybank

Magungunan hana ɗaukar ciki ya ƙaru zuwa kashi 27 cikin 100 a Najeriya – Gwamnati

Date:

Gwamnatin tarayya ta jaddada ƙudirinta na samun ƙarin masu amfani da magungunan hana daukar ciki zuwa kashi 27 cikin 100 nan da shekarar 2024.

Babban Sakatare a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Daju Kachollom, ce ta bayyan haka a wajen buɗe taron shekara-shekara na kwana biyu da ƙungiyar ‘Society Family Health’s (SFH) Adolescent 360’ (A360-Amplify) ta shirya, don ƙara nazari game da amfani da magungunan.

Taron na mai taken: “ɗorawa a kan nasarorin da aka cimma a shirin bunƙasa lafiyar balagar masu tasowa a Najeriya”

Kachollom, wadda Darakta a sashen kula da lafiyar iyali, Dakta Stella Nwosu ta wakilta, ta ce wannan matakin ba wai manufa ce kawai ba, amma alƙawari ne ga matasan kasar.

“Wannan alƙawari ne na ƙarfafa matasa da ilimi da kayan aiki don yanke shawara mai kyau game da lafiyar jima’i da haihuwa”.

“Wannan shirin zai ba da fifiko mai ƙarfi kan Tsarin Dan Adam (HCD) da haɗa kai cikin tsarin kiwon lafiya da ci gaba na gwamnati.

“Shirin ya samo asali ne ta hanyar fahimtar gamayyarmu cewa, za a iya samun tasiri mai ɗorewa ta hanyar hada kai don tabbatar da “ɗorawa a kan nasarorin da aka cimma a shirin bunƙasa lafiyar balagar masu tasowa a Najeriya” ba tare da wani tangarɗa ba cikin yanayin kiwon lafiya.

Kamfanin Dillancin Labarai na  (NAN), ya ruwaito cewa, taron ya ba da dama ga abokan tarayya da kuma masu ruwa da tsaki daga bangarorin gwamnati da masu zaman kansu don yin tunani kan sabbin hanyoyin da za a bi don dorewar shirin.

vanguard news nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp