Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci samun haɗin kai bayan da ƙyaftin Jarrod Bowen ya kalubalanci magoya baya a Molineux, bayan da Wolves ta yi waje da su a League Cup ranar Talata.
Da kansa Bowen ya je wajen zaman magoya baya yana tafa musu, sai aka ga ya harzuka kamar dai an faɗa masa wata wagana da ta ɓata masa rai.
West Ham ta kasa cin wasa uku da fara shiga gasar bana, wadda Sunderland ta doke 3-0 a makon farko da rashin nasara 5-1 a hannun Chelsea duk a Premier League.
Ranar Talata Wolverhampton ta doke West Ham 3-2 ta kuma yi waje daga Carabao Cup na kakar nan.
West Ham za ta je Nottingham Forest ranar Lahadi a wasan mako na uku a babbar gasar tamaula ta Ingila.