fidelitybank

Magoya bayan Tinubu sun fara fusata a kan takarar Osibanjo

Date:

Magoya bayan jagoran APC na kasa, Bola Tinubu, sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke kara samun karbuwa a takarar shugaban kasa a 2023 wanda a cewar su, mai yiwuwa shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shi.

A cewar Vanguard, majiyoyi a sansanin Tinubu sun damu da dama da jigogin APC zai samu a 2023, domin Osinbajo na iya zama dan takarar da Buhari ya ambata yayin hirarsa ta gidan talabijin na Channels.

Buhari dai a hirar ya ki bayyana sunan dan takarar sa a zaben shugaban kasa a 2023, ya na mai cewa mai yiwuwa a yi yunkurin yi wa dan takarar idan ya yi haka.

Koken na sansanin Tinubu ya zo ne a kan yadda babban goyon bayan da masu yi wa mataimakin shugaban kasa suke kara yi mikewa na neman shugaban kasa a 2023.

Amincewar ya bayyana musamman a Arewa kuma kwanan nan ya koma Kudu tare da jihar Delta a matsayin farkon kaddamarwa.

Sansanin Tinubu, wanda ya sha alwashin ba zai taso da batun fadar shugaban kasa ba, duk da haka, ya yi la’akari da yadda ake ambaton sunan Osinbajo tare da hasashe a ko’ina, domin zaben shugaban kasa a 2023 tare da maigidan sa, Buhari, acna kallon wata hanya.

“Ba za ka iya gaya mani cewa Shugaban kasa bai san komai a kan haka ba, kuma a na yi wa mataimakinsa aiki ya tafi ofishinsa, shi kuma jahili ne? A’a, a’a,” wani babban aminin Tinubu ya bayyana jiya.

Akwai kuma rahotannin da ke cewa, mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, ya musanta rahotannin da ke cewa Osinbajo, a ranar sabuwar shekara, ya ziyarci shugaban kasar ne domin neman albarkarsa a zaben shugaban kasa na 2023.

Da ya ke mayar da martanin rahotannin, ya ce Osinbajo ya tsaya tsayin daka wajen gabatar da ayyuka kamar yadda fadar shugaban kasa Buhari ta mika masa.

Sai dai kuma sansanin Tinubu ya ci gaba da kasancewa cikin rashin jin dadi kan abin da ake zarginsa da shi a matsayin wata manufa ta sirri inda majiyar ta ce, “Ta yaya ma’aikacin naku zai rinka tafiya haka kamar ka nada shi a ofishin ku? Kuna aika shi nan da can don fallasa shi?

“Idan ka na da mata sai ta yi rashin tarbiyya, ni wa zan yi korafi alhali kai mijin ba ruwanka? Don haka za mu ci gaba da sa ido.”

Da aka tambaye shi ko Osinbajo da Tinubu sun ga na ne kan ra’ayin mataimakin shugaban kasa, majiyar, wacce ya kamata ta sani, ta amsa a hankali, “Ban sani ba, amma ku sani.”

Sahara Repoters ta rwaito cewa, an gano cewa, damuwar sansanin Tinubu ya kara ta’azzara ne, sakamakon yadda jam’iyyar APC ta dage gudanar da babban taron kasa na zaben sabbin jami’an na kasa.

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp