Magoya bayan Bola Tinubu, sun yi kira ga mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da ya mika goyon bayansa ga Tinubu.
Tun da farko Osinbajo ya ja kunnen magoya bayansa kan kalaman batanci ga shugaban jamâiyyar APC mai mulki ta kasa.
Magoya bayan Tinubu sun bukaci mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo da ya janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa tare da marawa Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a 2023.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa, wani shugaban matasa a yankin Neja Delta, Mista John Dekawei ne ya yi wannan kira a Warri yayin zantawa da manema labarai. Ya ce ya kamata Farfesa Osibanjo ya kasance mai biyayya ga jagoran siyasarsa, wato Tinubu ta hanyar mara wa takararsa ta shugaban kasa baya.
Jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu, na ci gaba da tuntubar jiga-jigai kan fatansa na zama shugaban kasa a zaben 2023.