Sowa ta ɓarke a gaban zanƙaleliyar hasumiyar Eiffel Tower da ke birnin Paris daidai lokacin da ake bayyana hasashen cewa Emmanuel Macron ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a yammacin yau Lahadi.
Magoya baya sun yi ta ihun “Macron, shugaban ƙasa”.
Macron zai ci gaba da jagorancin Faransa cikin shekara biyar masu zuwa.