Rahotanni sun ce masu zanga-zanga fiye da 1000 ne suka nufi Kotun Koli da ke Abuja a ranar Litinin, don shigar da korafi a kan rashin gamsuwarsu da hukuncin Kotun Daukaka Kara, da ta soke nasarar ‘yan majalisar wakilai hudu na jam’iyyar adawa ta PDP daga jihar Filato.
Masu zanga-zangar karkashin jagoranci kungiyar Coalition for Justice in Africa, CJA dauke da rubuce-rubuce a kyallaye da alluna, sun gabatar da wasikar nuna baci rai ga Alkalin Alkalan Najeriya, Mai shari’a Olukayode Ariwoola.
A cewar masu zanga-zangar kotun daukaka karar, da hukuncinta, ta ruguza kudurin masu zabe na jihar Filato, lokacin da ta ayyana ‘yan takarar da suka fadi zaben ‘yan majalisar wakilai na ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin wadanda suka yi nasara.
A baya-bayan dai, magoya bayan jam’iyyar PDP na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a jihar Filato a kan hukuncin kotun daukaka kara da ya rusa zaben ‘yan majalisar wakilan PDP guda hudu.
Rahotanni sun ce kotun ta kafa hujjar rusa zabukan ne a kan takaddamar da PDP ta yi fama da ita, ta kafin zaben.