Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya karbi bakuncin mambobin jam’iyyar PDP sama da 250, wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a karamar hukumar Fune da ke jihar.
Da yake karbar wadanda suka sauya sheka, Gwamna Buni wanda mataimakinsa Idi Barde Gubana ya wakilta ya bayyana wannan ci gaban a matsayin babban rashi ga ‘yan adawa.
Ya kuma tabbatar wa da sabbin ‘yan jam’iyyar cewa jam’iyyar za ta ba su dama da dama kamar sauran mambobin, yana mai cewa “APC ta yi imani da dunkulewar Nijeriya daya, sabanin PDP”.
A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar na jihar, Mohammed Gadaka wanda ya taya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki murna, ya bukaci sauran ‘yan jam’iyyun siyasar jihar da su yi koyi da su domin ciyar da jihar gaba.
Wani tsohon mamba a jam’iyyar PDP a karamar hukumar Fune, Mallan Iliyasu Adamu Jilum wanda ya yi magana a madadin wadanda suka sauya sheka ya ce shawarar da suka yanke na sauya shekarsu ba zai zo a lokaci mafi kyau ba.
Jilum ya ce “Mun yi watsi da tsohuwar jam’iyyarmu ne saboda yadda Gwamna Mai Mala Buni ya jagoranci gaskiya.”
Muhimman abubuwan da suka faru a wajen bikin sun hada da mika tutocin jam’iyyar APC ga sabbin masu shigowa da mataimakin gwamnan jihar wanda shugaban jam’iyyar na jiha, Mohammad Gadaka ya marawa baya.