Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Zamfara, ta gargadi magoya bayanta da su daina barnata kadarori na jam’iyyar APC.
Sakataren jam’iyyar, Faruk Shettima Rijiya ya ce jam’iyyar PDP ta lashe zaben gwamna a jihar ba ta baiwa kowa ikon lalata kadarori na ‘yan adawa ko na daidaikun mutane ba.
A wata tattaunawa da ya yi a Gusau, ya ce, “Ba ma cikin irin wannan shiri kuma ba za mu taba goyon bayan irin wannan rashin adalci ta kowace fuska ba.
“Jihar Zamfara na bukatar a mayar da matsayinta ba wai a lalata dukiyoyin da ake da su ba, jam’iyyar ta nesanta kanta da duk wanda aka samu yana yin haka.”
Ya ce gwamnati mai zuwa ba ta da niyyar farautar kowa, inda ya ce rade-radin da ake ta yadawa a jihar na cewa Gwamna Bello Mohammed Matawalle ne ake kai wa hari, karya ne.
“Ba mu yiwa kowa hari ba amma duk wanda aka samu da laifin doka dole ne ya fuskanci sakamakon shari’a saboda babu wanda za’a mayar da saniya mai tsarki ko kuma wanda ba za a iya tabawa ba saboda sabuwar gwamnati ta shirya kama su.
“Rushe jam’iyyun adawa ko kadarori na daidaikun jama’a ba ya taimaka wa gwamnati mai zuwa a kowane mataki sai dai a bar magoya bayansu su ci gaba da biyayya ga jam’iyyar.