Magoya bayan tawagar Morocco da ke fatan zuwa kallon wasan kasar da Faransa a ranar Laraba, sun fuskanci ɓacin rana, yayin da aka soke wasu jiragen da ya kamata su yi jigilarsu da kuma matsalar ɓacewar tikitin jirgi.
Kamfanin jirgin kasar – Royal Air Moroc, ya soke tashin jirage bakwai a yau, yana mai ɗora laifin ga hukumomin Qatar.
Wasu ƴan ƙasar da suka riga suka isa Qatar sun ce babu tabbas kan dubban tikitin da hukumar ƙwallon Morocco ta yi alƙawari.
Morocco dai ta kasance ƙasa ta farko daga Afrika, kuma ta farko daga ƙasar Larabawa da ta kai zagayen dab da ƙarshe a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar.