Magoya bayan Manchester United sun shirya wata zanga-zangar nuna adawa ga mamallakan kulob ɗin kafin wasan United da Luton ranar Asabar a yayin da suke buƙatar a sayar da ƙungiyar.
Ƙungiyar magoya bayan United ta dakatar da adawa da dangin Glazer bayan mutuwar Sir Bobby Charlton.
Sai dai suna kira ga magoya bayansu da su hallara a kusurwar arewa maso yammacin filin wasan domin abin da suka bayyana a matsayin zanga-zangar lumana.
Wannan dai za ta kasance zanga-zanga ta farko tun bayan da aka bayyana cewa Sir Jim Ratcliffe na fatan sayen ƙaramin hannun jari a kulob ɗin, a wani mataki da ke nuna cewa dangin Glazer za su ci gaba da kasancewa masu rinjaye.
Bugu da ƙari, ana sa ran Ratcliffe zai sanya kusan fam miliyan 245 na kuɗinsa don yin aikin garambawul a filin wasan.
Majiyoyi da dama daga ciki da wajen United sun shaida wa BBC cewa dole ne a hanzarta gaggawar sauya ikon mallakar ƙungiyar, wanda aka ƙaddamar kusan watanni 12 da suka wuce, saboda rashin tabbas da ake fama da shi ba ya taimaka wa kociyan ƙungiyar Erik ten Hag.
United ta yi rashin nasara a wasa na tara cikin 17 a kakar wasan bana a Copenhagen kuma tana fuskantar yiwuwar ƙasa kai wa zagaye na gaba a gasar zakarun Turai.
Sau huɗu ne kawai suka kai zagaye na biyu a gasar tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya a shekarar 2013.