Wani gungun matasa ya yi dafifi a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi domin gudanar da zanga-zanga kan zargin an tafka maguɗi a zaben shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokoki a jihar.
Lamarin na zuwa ne yayin da hukumar zaɓe INEC ta sanar da sakamakon zaɓen sanatoci da na ƴan majalisar wakilai.
Waɗanda suka gudanar da gangamin sun haɗa da magoya bayan tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Sam Egwu da sauran magoya bayan ƴan takara kamar Micheal Amannachi da Linus Okorie da Laz Nweru Ogbe da Eze Emmanuel.
Sun yi zargin cewa an fara yin zaɓen cikin lumana amma daga bisani kuma labari ya sha banban inda maguɗi ya shigo ciki.
Masu zanga-zangar sun yi kira ga INEC da ta gaggauta ɗaukan mataki tare da sanar da sahihin sakamakon zaɓen da aka gudanar a yankunan Ebonyi domin kare afkuwar tashin hankali.
Mrs Paulin Onyekachi, Shugabar INEC a jihar ta Ebonyi, ta yi kira ga masu zanga-zangar da su rungumi zaman lafiya.