Magoya bayan Arsenal a Nairobi, babban birnin Kenya sun taru a wani coci domin yin addu’a ta musamman domin nuna godiya bayan da kungiyar ta lallasa Crystal Palace da ci biyar babu ko daya a wasan Firimiya da suka buga ranar Asabar.
Yayin taron addu’oin, magoya bayan sanye da rigunan Arsenal sun yi ta rera wakokin yabo tare da bayyana godiya ga kungiyar saboda bajintar da ta yi.
Sun kuma yi addu’oin ganin Arsenal ta dore kan wannan tafarki a gasar.
an jarida Kennedy Muriithi wanda daya ne daga cikin wadanda suka halarci taron addu’oin, ya wallafa hotunan a shafukan sada zumunta.
A yanzu Arsenal da Manchester sun yi canjaras a teburin gasar da maki 43 inda Liverpool ta sha gabansu da maki 5.
Hotunan sun janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta inda wasu suke zolayar magoya bayan na Arsenal.