fidelitybank

Magoya bayan Arsenal na cigaba da yin gunaguni bayan an yi musu bugun Sakwara

Date:

Magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal na ci gaba da bayyana ra’ayinsu kan rashin nasara da ƙungiyar ta yi a hannun Newcastle a wasan kusa na da ƙarshe a gasar Carabao.

Ƙungiyar dai ta yi rashin nasara da ci 2-0 da nema a wasan da suka kara a filin wasa na St. James’ Park.

Rashin nasarar da Arsenal ta yi a gidan Newcastle na nufin ta sha kaye da ci 4-0 gida da waje da suka buga a matakin wasan kusa da na ƙarshe na gasar.

Alhaji Yaman mai Arsenal ɗan asalin jihar Kano mazaunin Legas, ya ce wannan wasa bai yi musu ɗaɗi ba.

”Newcastle sun ci mutuncin Arsenal, a gidanmu sun ci mu 2-0, sannan a gidansu sun yi mana 2-0”.

”Wannan abin takaici ne yadda ƙungiyarmu ke kan ganiya a bana, amma a ce ko ƙwallo guda mun kasa ci a duka wasannin biyu, gida da waje”.

Shi kuwa Safiyan Mai Arsenal cewa ya yi wasan bai ba shi mamaki ba, la’akari da cewa tuna wasan farko Newcastle ta ci su 2-0 a wasan farko da aka buga a Emirates.

”Dama na san zai yi wahala mu je gidansu mu yi musu 3-0,” kamar yadda ya ce.

Ƙungiyar – da Mikel Arteta ke jagoranta – yanzu za ta mayar da hankali kan kofin Premier da take fatan lashewa, bayan da take mataki na biyu da tazarar maki shida tsakaninta da Liverpool ta ɗaya.

Haka kuma Gunners ɗin ta kai matakin wasan zagayen ‘yan 16 a gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Rabon da Arsenal ta ɗauki wani kofi dai tun 2020 lokacin da ta ɗauki kofin FA Cup.

latest news in nigeria today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp