Magoya bayan jam’iyyar APC, sun yi wani gangami a Abuja, domin nuna goyon bayansu ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Magoya bayan jam’iyyar sun ce, suna zaman dirshan din ne domin taya murna ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.
Sun kuma ce, sun taru ne domin tabbatar da cewa an rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa a ranar 29 ga watan Mayu.