fidelitybank

Magoya bayan APC ku kwantar da hankalin ku – Gwamnatin Kano

Date:

Jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ta yi kira ga mambobinta da magoya bayanta da su kwantar da hankulansu su kasance masu bin doka da oda ko da kuwa sakamakon bukatar da suka yi na sake duba zaben gwamnan jihar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi a ranar 18 ga watan Maris.

Karanta Wannan: Magoya bayan APC sun yi zaman dirshen a Abuja har sai an rantsar da Tinubu

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, inda ya kara da cewa a matsayinsu na masu hannu da shuni sun shahara wajen bin ka’ida.

Ya ce, Jam’iyyar za ta yi duk mai yiwuwa a cikin tanade-tanaden doka da sauran tsare-tsare don ganin an tabbatar da adalci a lamarin da kuma amincewa da bukatarsu ta sake duba zaben gwamnan da ya gabata.

Sanarwar ta bayyana cewa, Gwamna Abdullahi Ganduje da mataimakinsa da dan takarar gwamna, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakinsa, sun bayyana gamsuwarsu da yadda ‘yan jam’iyyar suka gudanar da kansu kafin zabe da lokacin da kuma bayan zabe.

the sun newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ĉ´ansandan jihar Kaduna, sun buĈ™aci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi Ĉ™ungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban Ĉ™aramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp