Sanata Albert Bassey Akpan ya fice daga jam’iyyar PDP, saboda rashin ba shi kafar tabbatar da aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a zaben 2023.
A cikin wata wasika da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta yayin zaman majalisar a ranar Laraba, Akpan ya godewa jam’iyyar PDP da ta bashi damar zama sanata a jamhuriyar tarayya.
Sai dai ya ce ba zai iya cimma burinsa na zama gwamnan jihar Akwa Ibom a kan dandalin jam’iyyar ba saboda shugabancin jam’iyyar a jihar tun da jam’iyyar ta samu ‘dan takara da aka fi so’ a zaben fidda gwani.
Sanata Akpan ya ce, ya ji kiran da magoya bayan sa suka yi na ya koma jam’iyyar matasa ta YPP domin ya cika burinsa na zama gwamnan jihar Akwa Ibom.
Da wannan ci gaban YPP na da Sanatoci biyu a Majalisar Dattawa mai ci yanzu.
Bassey Akpan dai yana wakiltar Akwa Ibom Arewa maso Gabas a Majalisar Dattawa tun shekarar 2015.