Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyya mai mulki a Najeriya, APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga al’ummar jihar Legas da su kwantar da hankalinsu sannan su guji duk wani abu da zai iya kaiwa ga karya doka da oda.
Tinubu ya ce bai kamata mutane su tayar da hankalinsu ba, bayan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na Legas ya nuna Jam’iyyar Labour ce ta yi nasara, inda ya ce tsarin dumukuraɗiyya ya bai wa kowa ikon zaɓar abin da yake so.
Tinubu ya bayyana haka ne cikin sanarwar da Bayo Onanuga, jami’in yaɗa labaran kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC ya fitar yau Litinin.
Tinubu ya kuma bayyana damuwa game da rahotannin tashin hankalin da aka samu a wasu sassan jihar.
Tsohon gwamnan na jihar Legas ya ce: “Bai kamata a samu tashin hankali ba kasancewar APC ta sha kaye a Legas da tazarar ƙuri’un da ba su taka kara sun karya ba.”
“Dama a tsarin dumukuraɗiyya, za ka yi nasara a wani wajen, ka sha kaye a wasu wuraren. Bai kamata mu kawo naƙasu ga tsarin sanar da sakamakon zaɓen ba,” in ji sanarwar.
A sakamakon wucin-gadi da aka fitar a matakin jiha, INEC ta ce dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar hamayya ta LP ya samu nasara a zaɓen da aka gudanar a Legas ɗin – birni mafi girma a Najeriya.
Shi ma Gwamnan jihar ta Legas, Babajide Sanwo Olu ya buƙaci mutane su kwantar da hankalinsu su kuma ci gaba da gudanar da harkokinsu na kasuwanci ba tare da wata fargaba ba.
Cikin sanarwar da ya fitar yau Litinin, Gwamna Sanwo-Olu ya ce, ya umarci hukumomin tabbatar da doka su sa ido domin hana afkuwar rikici a sassan jihar.
“Na kasance gwamnanku kusan shekara huɗu inda nake fifita zaman lafiya da son juna a tsakanin ƙabilu da mabiya addinai daban-daban ba tare da nuna wani banbanci ba.”
“Mu kwantar da hankalinmu, komai zai tafi lafiya lau. Mu mutane ne masu son zaman lafiya kuma hakan za mu ci gaba da kasancewa.” in ji Babajide Sanwo-Olu.