Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, a ranar Alhamis din da ta gabata, ta gano gawar wani mutum mai shekaru 49, tare da ceto wani yaro dan shekara 17 a rijiyar gidansa a garin Offa.
Mutumin mai suna Fasasi Afeez, da dansa Kaleed Afeez na Gaa Jangbo, Igbonna Road Offa, a karamar hukumar Offa ta jihar Kwara, sun fada cikin rijiya.
Sai dai yayin da aka tsinci gawar mutumin, an ceto dan da ransa.
A cewar kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Hassan Adekunle, lamarin ya faru ne da misalin karfe 04:11 na rana, kuma an gayyaci birgediya ta wayar tarho da wani Alhaji Taiye Gbadamosi da ke zaune a unguwar.
A cewar wani rahoto, “Yaron da aka ceto ya je diban ruwa daga rijiyar cikin gida, kuma ana cikin diban ruwa ne, sai ga wata kafarsa ta zame daga kasa, a karshe ya fada cikin rijiyar.
“Duk da haka, kafin isowar jami’an kashe gobara, mahaifinsa a lokacin da yake kokarin ceto wanda abin ya shafa, kwatsam kafafunsa sun zame daga kasa kuma daga karshe ya fada cikin rijiyar.”
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Prince Falade John Olumuyiwa, ya bayyana alhininsa game da faruwar lamarin, ya kuma bukaci jama’a da su kara kula da harkokinsu na yau da kullum, su guji tura yara masu karancin shekaru zuwa debo ruwa a rijiyoyin gida.