fidelitybank

Magidanci ya mutu a ramin Shadda wajen dako wayarsa da ta fada a Kano

Date:

Wani mutum mai suna Mu’azu Garba a jihar Kano ya mutu a lokacin da yake kokarin dako wayarsa da ta fada ramin shadda na bayi.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a garin Jigirya da ke karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Da yake bayyana lamarin, Abdullahi ya ce, hukumar ta samu wani kira a ranar Alhamis da misalin karfe 1:35 na rana daga wani Abbas Abubakar, inda ya ce, wani mutum ya makale a cikin ramin shadda.

Ya ce, mutumin mai shekaru 40 da haifuwa yana kokarin fito da wayarsa da ta fada cikin ramin, amma ya kasa fitowa daga cikin ramin.

“Nan da nan muka aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 1:45 na rana,” in ji Abdullahi.

Sai dai ya ce an fito dashi a macce, kuma an mika gawarsa ga hakimin unguwar Jigirya, Nuhu Adamu.

www.najnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp