fidelitybank

Magidanci ya kashe Matarsa bayan ta ƙi amince wa ya sadu da ita

Date:

An kama tsohon ma’aikacin hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Adamawa, Aminu Mahdi bisa zarginsa da dukan matarsa har lahira.

Aminu mai shekaru 63 da haihuwa kuma ya fito daga unguwar Yelwa da ke karamar hukumar Mubi ta Arewa, an zargi matarsa ta biyu, Hadiza Zubuchi, mai shekaru 46, saboda ta hana shi shiga gadon ta.

Wanda ake zargin wanda ya amsa laifin da ake zargin ya aikata, ya shaidawa ‘yan sanda cewa ba ya nufin matarsa ta mutu, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje ya bayyana.

Nguroje ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da manema labarai da yammacin ranar Alhamis, inda ya ce Aminu ya dawo gida ne da misalin karfe 9:00 na daren Lahadin da ta gabata, 27 ga watan Agusta, 2023, inda ya ci karo da lamarin da ya kai ga kashe matarsa.

Nguroje ya ce bayan Aminu ya ci abinci ya canza kaya, sai ya tafi dakin da zai kwana da matarsa, amma matarsa ta hana shi amfani da gadonta.

Da yake matar ba ta bari ya taba ta ba sai ta fara dukansa da sanda, sai ya kwace mata sandar ya yi ta dukanta.

Duka ya yi tsanani sosai har matar da ya aura a shekarar 2016 ta mutu daga karshe.

Cikin nadama yayin da yake shaida wa ‘yan sanda labarinsa, Aminu ya ce, “Ban yi tsammanin irin wannan lamari zai faru da ni ba. Kuskure ne.”

nigerian news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp