A ranar Litinin din da ta gabata ne mazauna garin Masaka da ke karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa suka shiga cikin firgici bayan da wani mutum mai suna Badejo Idowu ya daba wa dansa na farko mai suna Tunde Badejo wuka har lahira, bisa zargin mallakar wani fili mallakar dangin.
City & Crime sun samu labarin cewa, Tunde ya shafe sama da shekara guda yana cin zarafin mahaifinsa.
Matar marigayin Madam Tolani Badejo, ta ce, mijinta ya nemi Tunde da ya ba shi lokaci domin ya raba fili cikin adalci tsakanin sauran ‘yan uwa.
Ta bayyana cewa, “Ya kasance a wuyan mijina don filin tun bara. Don haka a gardamarsu ta karshe a ranar Litinin, ya zaro wuka ya daba wa mahaifinsa sau da yawa a kai, wuya, kirji, hannaye da kafafuwansa wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Na daga murya sai ya gudu.”
Dan marigayin na biyu, Ayomide Badejo, ya ce, an kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda yayin da aka ajiye gawar mahaifinsa a dakin ajiyar gawa. In ji Daily Trsust.