fidelitybank

Magidanci ya kai karar Matarsa bayan ta canja sunayen ‘ya’yan su zuwa na Masoyinta

Date:

Ayodeji Obayan, mai matsakaicin shekaru, a ranar Juma’a, ya garzaya kotun al’ada ta Grade ‘A’ da ke Oke-Eda, Akure, Jihar Ondo, inda ya nemi mahaifar ‘ya’yansa hudu da ta dawo da sunayen su kamar yadda yake a baya maimakon sabon masoyinta.

Matakin na zuwa ne bayan matar sa Lillian Obayan ta bayyana cewa ta sauya sunayen ‘ya’yansu domin ya dace da sunan sabuwar masoyinta.

Obayan, wanda ya nuna matukar bacin ransa kan lamarin, ya sha alwashin bin doka da oda domin tabbatar da hakkinsa a matsayin uban ‘ya’yansa.

A cewarsa, ya yanke shawarar garzaya kotu domin neman taimakonta biyo bayan matakin da matarsa ta dauka na sauya sunayen ‘ya’yansu ba tare da izininsa ba.

A lokacin da ya ke ba da shaida a gaban kotu, Obayan ya bayyana cewa auren nasu da ya shafe shekaru 23 yana fama da rikici da cin zarafi akai-akai.

Ya bayyana cewa a cikin 2019, Lillian ta kwashe kayanta kuma ta bar gidansu don shiga tare da wani mutum.

A cewarsa, abin da ya kara ta’azzara shi ne, matar da ya rabu ta canza ba kawai sunanta ba, har ma da sunayen ‘ya’yansu domin ya dace da sunan sabon masoyinta.

A nata bangaren, Lilian ta bayyana Obayan a matsayin wanda ba shi da alhaki, “Obayan ba mijin kirki ba ne a gare ni, kuma uba nagari ga ’ya’yansa, domin ba ya biyan kudin makaranta, kuma ba ya kula da yadda suke rayuwa.

“Bai biya sadakina ba. Don haka, daga karshe na sami namiji da zan aura. Kuma sabuwar soyayyata tana son ’ya’yana su riƙa ɗaukan sunansa maimakon na ubansu mara nauyi.

“Yaranmu sun isa zabar wa kansu tunda ba yara ba ne. ’Yan mata biyu na farko, Mayomi da Damilola, ‘yan shekara 22 da 20, yayin da yaran maza, Ariyo da Aduragbemi, ‘yan shekara 18 da 16 ne.”

A halin da ake ciki, a hukuncin da ya yanke, shugaban kotun, Majistare Olusegun Rotiba, ya roki bangarorin da su bar zaman lafiya ya wanzu a tsakaninsu.

Daga baya ya dage sauraron karar har zuwa ranar 28 ga Satumba, 2023, don ci gaba da karbar adireshi na baka da kuma yiwuwar yanke hukunci.

daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp