Ana zargin wani mutum mai shekara 32 da kashe matarsa mai suna Mercy Samuel a Jos a jihar Filato.
Hukumomin jihar Filato sun tabbatar da faruwar lamarin, inda Kwamishiniyar kula da harakokin mata ta jihar Rebecca Sambo ta shaida wa BBC Pidgin cewa, lamarin ya faru ne a daren 17 ga watan Afrilu.
Ta ce mijin ya yaga cikin matarsa misalin ƙarfe biyu na dare ya cire ƴan hanjinta.
Matar ƴar shekara 25 ta mutu bayan an garzaya da ita zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Bingham a Jos domin yi mata tiyata.
Rundunar ƴan sandan Filato ta ce tana kan gudanar da bincike game da al’amarin.
Mercy da mijinta sun yi aure tsawon shekara tara kuma sun haifi ƴaƴa biyu.
Dan uwanta ya ce cikin dare makwabta suka ji tana ihu, ko da aka fito sai ga ƴan hanjin cikinta a hannunta.
Yanzu haka ƴan sanda na farautar mijin wanda ya gudu.