Rundunar ‘yan sanda a Kano, ta tabbatar da mutuwar mata da miji a gidansu.
Ma’auratan sun gamu da akalin su ne a kauyen Kwa da ke karkashin karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar.
Ana kyautata zaton ma’auratan sun mutu ne sakamakon shakewar hayakin gawayi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna-Kyawa ya bayyana wadanda suka mutun a matsayin Sulaiman Idris mai shekaru 28 da Maimuna Haliru mai shekaru 20.
PRO ya ce bayan babu wanda ya ji ta bakinsu, kakar Idris ta tilastawa bude kofa, ta tarar da su biyun ba su da motsi.
Tawagar jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin CSP Ahmed Hamza DPO DPO na Dawakin Tofa sun zarce zuwa wurin.
An garzaya da gawarwakin zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammed inda wani likita ya tabbatar da mutuwar su.
Haruna-Kiyawa ya lura cewa, ma’auratan sun kunna wutar ts gawayi don dumama dakin saboda yanayin sanyi.
Kakakin ya kara da cewa, “Sun kulle kuma hayakin da ke fitowa daga garwashin gawayi ya shafe su,” in ji kakakin.