Gwamnatin India ta ce, hudu daga cikin magungunan tarin da suka kashe wasu yara a Gambiya an yi gwaji an gano ba su da matsala.
Hukumar Lafiya Ta Duniya a watan Oktoba ta ce hudu daga cikin magungunan tari da kamfanin Maiden da ke da alaka da mutuwar yara 66 a Gambiya.
Daga baya hukumar kula da magunguna ta Indiya ta ce WHO ba ta da wata hujja ta wannan ikirari da ta yi. Indiya dai ita ce kasar da ta fi kai maguguna nahiyar Afrika.
Har yanzu dai ana ci gaba da bincike domin gano matsalolin da ke tattare da wadannan magunguna da suka janyo illa a Gambiya.