Magajin garin San Pedro Huamelula da ke ƙasar Mexico ya auri kada.
Victor Hugo Sosa ya auri kadar ce don ɗabbaka tsohuwar al’adar da iyaye da kakanninsa suka shafe shekara 230 suna yi.
Al’ummar yankin na San Pedro Huamelula sun yi imanin cewa aure tsakanin mutum da kadan zai kawo alkairai kamar damuna mai albarka da kyakkyawan amfanin gona.
Bikin ya gudana a ranar Juma’a a gaban mutane. In ji BBC.