Gwamna jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya magantu a kan wanda ya cancanci ya gaje shi a zaben 2023.
Badaru ya ce, ya zama dole duk wanda zai dare kujerar gwamnan jihar ya zamo mutum mai tawali’u, rashin son kai da kuma sauraron jama’a.
Ya bayyana hakan ne bayan ya amsa gayyatar wata kungiya mai zaman kanta ta Hadejia Ina Mafita.
Da yake bayyana cewa, hakkin mutanen jihar Jigawa ne su yanke shawara kan wanda suke so ya zama gwamnansu a 2023, gwamnan ya ce, “Ya zama dole wanda zai gaje ni ya zama mutum mai sauraron mutanen jihar Jigawa”. In ji Badaru.