Batun albashin ma’aikatan a jihar Borno ya ja hankali a kafofin sada zumunta a Najeriya inda aka riƙa yaɗa sakon banki da ke nuna kuɗi ƙasa da naira 10,000 wasu har 4,000 da wasu ma’aikatan jihar ke karɓa a matsayin albashi.
Wani mutum da BBC ta zanta da shi ya ce ya kwashe sama da shekara 10 ya na aiki a matsayin ma’aikacin gwamnatin jihar ta Borno amma har yanzu albashinsa bai wuce naira 15,000.
Ya ce hakan na faruwa ne duk kuwa da cewa karatunsa ya kai matakin digiri na biyu, duk da dai a farko an ɗauke shi aiki ne da takardar shaidar kammala sakandare.
Ya bayyana wa BBC cewa “mutane na cikin hali na ha’ula’i, ma’aikata na kwashe kwana 30 suna jiran albashi amma a ƙarshe sai a ba su 15,000 ko 8,000 ko 7,000”.
Sai dai ya ce hakan ya samo asali ne tun gwamnatocin da suka gabata.
A ɓangare ɗaya, gwamnatin jihar Borno ta ce ma’aikatan da ba su ƙware ba ne ke samun ƙaramin albashi.
Kwamishinan ilimi na jihar, Injiniya Lawan Abba Wakilbe ya ce “duk wani ƙwararren malami muna biyan shi albashi da kyau, waɗanda ake biya irin wancan albashi ba ƙwararru ba ne, kamata ya yi a ce mun sallame su”.
Ya ce “masu NCE satifiket muna biyan su naira 52,000, BEd kuma daga 60,000 zuwa sama, waɗanda kuma suka yi nisa muna biyan su 100,000 har ma sama da haka”.