Wasu mafarauta a yankin Benuwe sun ceto wani jariri da aka ce binne shi da ransa a karamar hukumar Buruku ta jihar.
A cewar wani mazaunin yankin, wanda kawai ya bayyana kansa da Terna, lamarin ya faru ne a unguwar Ashav Kusuv.
Ya bayyana cewa mafarauta ne suka gano jaririyar suka kawo ta da rai daga dajin da aka binne ta da ranta.
“Wasu mafarauta a ranar Asabar sun gano wata jaririya, suka ce sun same ta a binne da ranta a wani daji.
“A halin yanzu ana kula da jaririn a unguwar Ashav Kusuv,” in ji shi.
Shugaban karamar hukumar Iorkyaan Aberg, da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadi, ya tabbatar da labarin, inda ya bayyana cewa wasu mafarauta ne suka gano jaririn a wani daji.
Agba ya bayyana cewa, “Hakika wasu mafarauta sun sami jariri a cikin dajin amma muna kan bincike don sanin wanda ya je ya jefar da jariri a cikin dajin da kuma dalilin yin hakan.”
Har zuwa lokacin da ake wannan rahoto, kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Binuwai, Catherine Anene bai yi nasara ba, yayin da wayarta ta ci karo.