Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya bayyana ‘yan wasa masu karfi da suka hada da Karim Benzema da Luka Modric da za su kara da Eintracht Frankfurt a wasan karshe na cin kofin UEFA Super Cup na ranar Laraba.
Ancelotti ya fitar da ‘yan wasan ne a wani sakon da ya wallafa ta shafin intanet na Real Madrid ranar Talata.
Kungiyar Ancelotti ta lashe gasar zakarun Turai a kakar wasan da ta wuce, yayin da Frankfurt ta lashe kofin Europa.
Za a yi wasan karshe na cin Kofin UEFA Super Cup tsakanin Real Madrid da Frankfurt a filin wasa na Olympics na Helsinki kuma za a take wasa da karfe 8 na dare.
Ga ‘yan wasan Real Madrid da Frankfurt:
Masu tsaron gida: Courtois, Lunin, Luis López.
Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger, F. Mendy.
‘Yan wasan tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., Tchouameni, D. Ceballos, Camavinga.
Masu wasan gaba: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.