Rahotonni daga kasar Indonesiya na cewa wata mesa ta kashe tare da hadiye wata mata a lardin Jambi na kasar.
lamarin ya faru ne ranar Lahadi da safe lokacin da matar mai suna Jahrah, mai shekara 50, ta tafi wajen sana’arta ta diban ruwan karo a wani daji da ke bayan gari.
Bayan da iyalanta suka fahimci ba ta dawo ba, sai suka fara nemanta, inda bayan kwana guda wasu mazauna kauyensu suka ga wata mesa mai katon ciki a bayan kwance a bayan kauyen.
Inda nan take suka kashe ta, tare da farka cikinta suka kuma sami gawar matar a cikin mesar.
Shugaban ‘yan sandan lardin ya shaida wa kafafen yada labaran kasar cewa ”an samu gawar matar wadda ta fara kumbura a cikin mesar”.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da mesa ke kashewa tare da hadiye mutane a Indonesiya ba.
A shekarar 2017 da 2018 ma dai an samu irin wadannan rahotonni.