Sanata Aishatu Binani ta zama ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Adamawa.
Ta samu kuri’u 430 inda ta doke abokin hamayyarta Nuhu Ribadu wanda ya samu kuri’u 288.
Sanatan mai wakiltar Adamawa ta tsakiya a majalisar dattawa ta na daya daga cikin mata na farko da suka nemi kujerar gwamna. Za kuma ta yi niyyar zama mace ta farko da aka zaba gwamna a tarihin Najeriya.