A yau Lahadi za a fara gasar Kofin Duniya ta 2022 a Qatar, inda tawagogin ƙasashe 32 za su ɓarje gumi wajen ɗaukar kofin.
Su kuwa alƙalan wasa mata irinsu Salima Mukansanga ta ƙasar Rwanda, ita ce mace ta farko daga Afirka da za ta yi alƙalanci a gasar.
Tana cikin mata uku da za su yi busa a karon farko a tarihin gasar Kofin Duniya wadda ta maza ce.