‘Yar takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Republican, Nikki Haley, ta yi nasara a zaben fidda gwani, sai dai dole ta yi nasara kan daukacin wakilan jam’iyyarta a gundumar birnin Washington DC.
Mis Haley ta ce ba ta yi mamakin zabarta da ‘yan Republican suka yi ba, da watsi da tsohon shugaban kasar Donald Trump da tada kurar da ya yi.
Har yanzu Mr Trump ne ke sahun gaba a zaben fidda gwanin jam’iyyarsu, ana kuma sa ran zai samu karin wakilan da za su mara masa baya cikin makon da sauran jihohi za su zabi gwaninsu.