fidelitybank

Mace ta kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Filato

Date:

Wata mata mai suna Lucy Tapnang, ‘yar shekara 29 da haihuwa ta kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tare a Filato.

Matar wadda wasu ‘yan bindiga suka sace tare da wasu mutum uku, ta yi ta maza inda ta kwace bindiga samfurin AK47 daga hannun daya daga cikin wadanda suka sace su, to amma duk da haka sai da suka ji mata rauni da wuka.

Lucy wadda mazauniyar Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ce, na kan hanyarta ne ta zuwa karamar hukumar Mangu tare da wasu fasinjoji bakwai a cikin motar, a nan ne ‘yan bindiga suka tare su.

Lucy ta shaida wa shalkwatar ‘yan sanda da ke Jos cewa, lamarin abin tsoro da tashin hankali ne.

Ta ce,” A dai dai lokacin da muka kusa isa makarantar kimiyya ta Kuru, sai kawai muka ga wasu mutane sun tsayar da motar da muke ciki.Nan na ga wani mutum da bindiga a cikinsu yana kuma umartar duk mutanen motar mu sauka muka kuma mika wayoyin salularmu da kudi.A lokacin sai kawai na ce da fasinjojin motar ku fa maza ne yakamata mu yi ta maza don mu ceci kanmu, to amma sai suka ce mini ai mutanen na da bindiga kada su illatar da su.”

To daga nan ne ita ta yi mazan ta wufce bindigar da ke hannun daya daga cikin masu satar mutanen in ji mai magana da yawun ‘yan sanda jihar Alfred Alabo, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce, sauran fasinjojin ma sun taimaka mata bayan da suka ga ta kwace bindigar mutum guda.

Jami’in dan sandan ya ce ko da suka samu labarin harin sai suka aika jami’ansu ba tare da bata lokaci ba aka ceto mutanen.

daily post nigeria today news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gobara na cigaba da lakume wasu yankunan Turai

Gobarar daji na ci gaba da ruruwa a sassan...

An kama Fursunoni 7 da suka tsere daga gidan kurkukun jihar Nasarawa

Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya ta ce...

Gwamnati za ta gina titin jirgi a jihohi shida

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta haÉ—a gwiwa da...

Tinubu ya na cikin koshin lafiya – Farouk Adamu Aliyu

Tsohon É—an majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Faruk Adamu...

Amurka ta saka ladan dala miliyan biyar a kamo jagoran ‘yandaban Haiti

Amurka ta sanya dala miliyan biyar a matsayin lada...

Gwamnati ta janye karar da ta shigar kan Fasinjar jirgin Ibom

Gwamnatin Tarayya ta janye ƙarar da ta shigar kan...

Na so komawa Manchester United a 2012 – Lwandowski

Ɗanwasan gaban ƙungiyar Barcelona ta Spain, Robert Lewandowski ya...

Isak ya dage sai ya koma Liverpool

ÆŠanwasan gaba Alexander Isak ya nace sai ya bar...

Sadiq Umar da Bello El-Rufai sun sayi ƙungiyar Ranchers Bees ta Kaduna

ÆŠanwasan tawagar Super Eagles ta Najeriya da Real Socieded...

Atiku zai iya guduwa daga ADC ya koma PDP idan Jonathan ya tsaya takara – Diran

Tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa,...

Zoben matar Ronaldo ya kai dala miliyan 5 – Masana

Masana sun yi kiyasin tsadar zoben da Cristiano Ronaldo...

Kama Tambuwal ya na da alaka da shigarsa cikin hadakar jam’iyya – Atiku

Tsohon É—antakarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce kama...
X whatsapp