fidelitybank

Mace ta haifi jarirai huɗu lokaci guda a Zamfara

Date:

Wata mata a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta haifi jarirai hudu rigis a lokaci daya, wadanda dukkanninsu mata ne, a babban asibitin Shinkafi.

A bayanin da daya daga cikin ma’ikatan asibitin da suka karbi haihuwar, ungozoma Hajiya Kulu ta yi wa BBC ta ce, tun da farko hoton cikin da aka dauka ya nuna cewa matar na dauke da jarirai uku ne.

Amma kuma bayn da ta haifi ukun sai aka ga cewa akwai alamun karin na hudu, wanda shi ma ta haife shi.

Jami’ar ta ce dukkanin jariran da mahaifiyar tasu suna nan cikin koshin lafiya, amma kuma ta ce akwai matsalar da ake fuskanta, saboda ya kamata a sa su cikin kwalba amma kuma asibitin ba shi da wannan na’ura.

Hakan dai ya kasance wani kaluble a garesu domin iyayen masu karamin karfi ne, in ji ungozomar.

Mahaifin jariran, Mallam Is’haqa Isa, ya bayyana wa BBC cewa yana godiya ga Allah da Ya azurta shi da wadannan yara.

Amma kuma ya ce, yana neman taimako daga jama’a kasancewar ba shi da ko naira dubu biyar a halin yanzu, hasali ma ba shi da aikin yi, sannan kuma gurgu ne shi.

naija news legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ina nan a PDP na ban gudu ba – Adeleke

Gwamnan jihar Osun, ya musanta rahotonnin da ke cewa...

Tinubu ya isa birnin Rio na Brazil don halartar taron BRICS

Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa birnin Rio de...

Matakan da muke ɗauka kan kisan matafiya a Plateau – Mutfwang

Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato, ya ce gwamnatinsa...

Tinubu ya gaji tattalin arziki da ya kusa durkushewa – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyeson Wike, ya ce...

Har yanzu PDP tana nan da ƙarfinta – Isa Ashiru

Yayin da fagen siyasar Najeriya ke ci gaba da...

An kama ɗan shekara 70 kan zargin kashe ƙanwarsa a Jigawa

Rundunar ƴansandan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ta...

Ahmed Musa za ma sabon shugaban gudanarwar Kano Pillars

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa kyaftin...

Netherlands da Jamus sun zargi Rasha da aiki da makamai masu guba a Ukraine

Hukumomin leƙen asirin ƙasashen Netherlands da Jamus sun zargi...

Kotu ta bayar da umarni Majalisa ta dawo da Sanata Natasha

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta buƙaci...

Sojoji sun hallaka ƴanbindiga da dama a Plateau

Rundunar sojoji ta ce, ta kashe ƴanbindiga da dama...

Duk wani tuggun ku Atiku da El-Rufa’i ba za ku iya kayar da Tinubu ba – Bwala

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da kokarin da...

Mutuwar Dantata ta girgiza kasa baki daya – Tinubu

Shugaban kasa Ahmad Bola Tinubu ya bayyana Alhaji Aminu...
X whatsapp