An kama wata mai suna Blessing bisa zargin ta da kashe danta dan wata 11 a kauyen Ugep, da ke karamar hukumar Yakurr na jihar Cross River.
Jaridar PUNCH ta ce, jami’an ‘yan sanda sun isa wurin da lamarin ya faru ne daidai lokacin da matasa ke kokarin lakada wa matar duka.
Lokacin da ya tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya ce yanzu haka matar tana hannun hukuma.
Ugbo ya kara da cewa “ana ci gaba da bincike domin gano dalilin da ya sa ta yanka yaron, amma labarin da muka samu shi ne tana da tabin hankali.”