Wata daliba ‘yar shekara 16 daga makarantar Kano Capital Girls da ke jihar Kano, Hauwa’u Ibrahim Muhammad a ranar Larabar da ta gabata ta zama mace ta farko da ta zama shugabar majalisar yara ta Kano karo na hudu.
Hauwa’u, dalibar SS 2 daga karamar hukumar Nassarawa ta samu nasarar lashe zabe, bayan ta samu kuri’u 38 yayin da babban abokin hamayyarta, Sadiq Muhammad Ghali daga GSS, Gwale ya samu kuri’u 30.
Musa ya ce adadin yara 81 ne suka yi rajista kuma suka kada kuri’a a zaben.
“Akwai mukamai 10 da aka zaba. Muna da adadin mutane 81 da suka yi rajista da masu kada kuri’a a lokacin zaben.
Sauran manyan hafsoshin da aka zaba sun hada da, Mustapha Sunusi Sani a matsayin shugaban majalisar wakilai, Habiba Aliyu (Mataimakin shugaban majalisar wakilai), Muhammad Yasin (shugaban masu shari’a), Hamza Nasiru Ado (mataimakin shugaban masu shari’a), Ummulkhair Mahmud (Malaci), Ibrahim Abdullahi (Mataimakin Clerk), Hauwa’u Nasir Nuhu da Hassan Abubakar a matsayin Mace Bearer da mataimakiyar Mace Bearer bi da bi.
Yaran da suka fito daga makarantun gwamnati na kananan hukumomi 44 na jihar kuma masu shekaru tsakanin 12 zuwa 16 ne suka hallara, domin zabar manyan jami’ansu da za su jagoranci harkokin majalisar yara na tsawon shekaru uku masu zuwa.
Gwamnatin jihar Kano ce, ta shirya zaben tare da goyon bayan Expanding Social Protection for Inclusive Development, ESPID and Rule of Law and Anti-Corruption, RoLac. A cewar Vanguard.
A jawabinta na karba, sabuwar kakakin majalisar, Hauwa’u Ibrahim Muhammad ta yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukanta na shugaban majalisar.
Ta kuma yi alkawarin cewa, shugabancinta zai inganta kan halin da kananan yara ke ciki a jihar.