Ana cigaba da tantance masu kaɗa ƙuri’a da kuma dangwala ƙuri’a a wasu rumfunan zaɓe tun da misalin 8:30 na safe.
Wasu daga cikin rumfunan zaɓen da wakilan BBC suka ziyarta a Ado-Ekiti musamman mazaɓar Oke-Inyimi, tuni aka fara zaɓe a rumfa mai lamba biyu da mai lamba uku da huɗu da shida.
Owolabi Comfort ita ce mace ta farko da ta soma zaɓe a rumfa mai lamba biyu.
Ana amfani da sabuwar na’urar Bvas wurin tantance masu zaɓen.
Na’urar Bvas wato Bimodal Voter Accreditation system, an soma amfani da ita ne a zaɓen gwamna a Anambra a 2021 duk da cewa an samu tangarɗa a wasu wuraren.
Sai dai a zaɓen Ekiti, hukumar ta INEC ta ce za sake inganta na’urar ta Bvas inda ta ce tana sa ran za ta yi aiki da kyau.