fidelitybank

Ma’aikatu da kungiyoyi ku zama cikin shirin ko-ta-kwana – Kungiyar Kwadago

Date:

Bayan kama shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Joe Ajaero, kungiyar ta sanya dukkan ma’aikatan Najeriya da sauran kungiyoyin kwadago su zama cikin shirin ko-ta-kwana.

Jami’an tsaro na farin kaya, DSS, sun kama Ajaero a safiyar ranar Litinin.

An dauke shi ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe International Airport, Abuja, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa kasar Ingila, domin gudanar da aiki a hukumance, sai jami’an DSS suka dauke shi.

A wata sanarwa da ta fitar a hukumance X, NLC ta bukaci a gaggauta sakin shugabanta na kasa.

“Muna bukatar a gaggauta sakin shugaban majalisar, Comrade Joe Ajaero ba tare da wani sharadi ba,” kamar yadda ta rubuta.

Kungiyar ta kuma bukaci dukkanin kungiyoyin da ke da alaka da su, da majalisun jihohi, da kungiyoyin farar hula da kuma duk ā€˜yan Najeriya masu kishin kasa su kasance cikin shiri.

A kwanakin baya rundunar ā€˜yan sandan Najeriya ta gayyaci shugaban kungiyar ta NLC domin amsa tambayoyi kan zargin alaka da bayar da kudaden ta’addanci da dai sauran laifuka.

Kungiyar, bayan gayyatar, ta sha alwashin rufe tattalin arzikin kasar idan aka kama Ajaero.

nigerianewspapers.com.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ę“ansandan jihar Kaduna, sun buʙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ʙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ā€˜Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ʙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ā€˜yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp