Festus Keyamo, ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, ya karanta dokar ayyukan hukumar ga shugabannin zartarwa a karkashin ma’aikatarsa kan bukatar aiwatar da kashi 100 cikin 100.
Ya kuma nemi goyon bayan masu ruwa da tsaki a harkar domin kare aikinsa.
Keyamo ya bayyana hakan ne a kwanan baya yayin wani taron masu ruwa da tsaki na kwana daya a Legas.
A cewarsa, dole ne kowani hannu ya kasance a kan bene domin gudun kada shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kore shi.
“Mun yi zaman kwana uku tare da Shugaban kasa, dukkan ministocin sun hallara. Mun sanya hannu kan yarjejeniyar aiki. Na kuma rattaba hannu kan takardar aikina a jiya. Don haka, idan ba ku son a kore ni a cikin ‘yan watanni masu zuwa, dole ne ku tallafa mini.
“A wannan bangaren, ko dai a kore ni, ko kuma a kore su. Don haka, tsere ne ga wanda zai tsira. Abin da na gaya wa shugabannina ke nan: Dole ne wani ya mutu da farko, amma kafin in mutu, zan ɗauke ku.”
Wannan ci gaban dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ministoci a wani taron kwanaki uku da majalisar ministocin ta yi a Abuja.