A ranar Litinin din nan ne ma’aikatan wutar lantarkin suka rufe kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO), sakamakon rashin biyan su kudaden fansho da aka cire a cikin watanni 72 da suka gabata.
Ma’aikatan da ke karkashin kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE) sun sha alwashin ci gaba da rufe kamfanin har sai an tabbatar da kudaden da aka tura su kuma an biya su.
Shugaban kungiyar na shiyyar Arewa maso Yamma, Ado Ririwai, a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya bayyana cewa ma’aikatan ba za su sake bari a ci gaba da irin wannan hali na rashin kyau ba.
Ririwai ya zargi KEDCO da cin zarafin shugabannin kungiyar da ke kokarin yin magana a madadin ma’aikatan.
“Wannan aiki na mulkin mallaka ne; haƙƙin ma’aikata ne su yi yaƙi da abin da yake nasu,” inji shi.
Shugaban kungiyar ya kuma zargi kamfanin da kin bai wa ma’aikatan kiwon lafiya na asali “duk da hadurran da ke tattare da ayyukansu.”


