fidelitybank

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Date:

Ma’aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution Company (AEDC), sun yi barazanar tsunduma yajin aiki saboda abin da suka ce rashin biya musu buƙatunsu.

Kamfanin na AEDC na samar wa Abuja babban birnin Najeriya wuta, da kuma jihohin Nasarawa da Kogi da Neja masu maƙwabtaka.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata wasiƙa da ƙungiyoyin ma’aikatan biyu suka aike wa mahukuntan kamfanin domin sanar da su aniyarsu, suna masu cewa “yajin aikin zai iya farawa a kowane lokaci”.

“Ku tuna cewa mun ƙulla yarjejeniya da ku a ranar 27 ga watan Satumban 2024 domin jingine yajin aiki game da rikicin kasuwanci da suka shafi ma’aikata,” kamar yadda jaridar ta ambato wasiƙar na bayyanawa.

“Muna tunasar da ku matsalar ƙin biyan fanshonmu da aka cire mana tsawon wata 16, da ƙin fara biyanmu sabon mafi ƙarancin albashi, da ƙin ƙara wa ma’aikata matsayi tsawon shekara 10, da ƙin tabbatar da ma’aikata na wucin gadi a matsayin cikakku.”

today nation

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp