Ma’aikatan wucin gadi na hukumar kidaya ta kasa, NPC, sama da 300, sun yi zanga-zanga a ranar Laraba a Kano, sakamakon rashin biyansu alawus-alawus na horo na kwanaki 18 da ya kamata a yi a watan Fabrairun 2023.
Ma’aikatan sune waɗanda aka ɗauka don ƙidayar 2023.
Kakakin ma’aikatan wucin gadi na jihar, Aliyu Rulwanu, ya zargi hukumar da zabin biyan albashi wanda ya saba wa yarjejeniyar da suka kulla.
A cewarsa, ma’aikatan wucin gadi da ba a biya su albashi ba, sun rubuta wasiku da dama, inda suke tunatar da su alawus-alawus din da ya kamata a biya su da kuma neman a biya su cikin gaggawa, amma hukumar ta yi gum da bakinsu saboda babu wasu kalamai na karfafa gwiwa.
Ya ce ba su da wani zabi illa su shiga zanga-zangar lumana, suna neman kudadensu. A cewar wani ma’aikatun wucen gadi.
Jami’ar hulda da jama’a na hukumar kidaya ta jihar Kano, Hajia Jamila Abdulkadir Sulaiman, ta ce ma’aikatan wucin gadi ba su cika fom dinsu daidai ba, wanda hakan ya sa aka samu tsaiko wajen biyan alawus-alawus din da hukumar ke ci gaba da gyara kura-kuran da aka samu. .
Ta shawarci duk ma’aikatan wucin gadi da ba a biya su albashi ba da su yi hakuri, domin za a biya su alawus-alawus da zarar hukumar ta kammala gyara.